Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Afirka Ta Kudu: Putin Ya Taya Ramaphosa Murnar Nasara


Shugaban kasar Russian Vladimir Putin da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban kasar Russian Vladimir Putin da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa

Shugaban fadar Kremlin ta Rasha, Vladimir Putin ya taya takwaransa na Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa murnar sake lashe zabensa a matsayin shugaban kasa a Litinin din data gabata.

Hakan ya nuna alamar dorewar kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu duk da rashin tabbas din da ake dashi akan mamayar da rashan ta yiwa Ukraine tsawon fiye da shekaru 2 da rabi.

Putin da Ramaphosa
Putin da Ramaphosa

Sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon fadar kremlin dake ruwaito wayar tarho din da Putin ya bugawa Ramaphosa na cewar, "An bayyana fatan ci gaba da gudanar da ayyukan hadin gwiwa kan kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Rasha da Afirka ta Kudu a dukkan fannoni,"

Majalisar Dokokin kasar ce ta sake zaben Ramaphosa a Juma'ar data gabata. Saidai gazawar jam'iyyarsa ta African National Congress ta samu rinjaye a zaben watan daya gabata, karon farko cikin shekaru 30, ya sabbaba kafa gwamnatin gamin gambizar jam'iyyu biyar.

Kasashen Rasha da Ukraine sun yi ta sintirin neman samun goyon bayan kasashen Afrika tun bayan mamayar 2022, inda ministocin kasashen wajensu ke rangadi zuwa kasashen nahiyar.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG