Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi Magana Da Fati Ibrahim Attahiru, Sauran Iyalan Sojojin Da Suka Rasu


Hajiya Fati Ibrahim Attahiru (dama) lokacin da Aisha Buhari ta kai mata ziyarar ta'aziyya (Twitter/@Aishambuhari)
Hajiya Fati Ibrahim Attahiru (dama) lokacin da Aisha Buhari ta kai mata ziyarar ta'aziyya (Twitter/@Aishambuhari)

Ganawar na zuwa ne yayin da Najeriya ta fara makokin kwana uku da hutun kwana daya da aka ba dakarun kasar saboda rashin sojojin da aka yi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da mai dakin marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, Hajiya Fati Ibahim Attahiru da sauran iyalan sojojin da suka rasu a hatsarin jirgin da ya faru a Kaduna.

Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10 sun rasu a ranar Juma’a bayan da jirginsu ya fadi da yammacin ranar Juma’a a jihar ta Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

A ranar Asabar aka yi jana’izarsu a Makabartar dakarun kasar da ke Abuja.

“Da wannan yammaci (Lahadi,) Shugaba Buhari ya yi magana da mai dakin marigayi babban hafsan sojan Najerya Fati Ibrahim Attahiru, da sauran iyalan sojojin da suka mutu.” Mai ba Buhari shawara kan sha’anin kafafen sada zumunta na zamani Bashir Ahmad ya ce.

Ganawar shugaban da iyalan mamatan, na zuwa ne yayin da wasu ‘yan Najeriya ke nuna rashin jin dadinsu, kan yadda Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suka kauracewa wajen jana’izar sojojin.

Ko da yake, fadar shugaban kasar ba ta fadi dalilin rashin zuwan shugaban da mataimakinsa ba.

Amma a ranar Lahadin, uwargidan Buhari, Aisha Buhari ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Attahiru.

“Na kai ziyarar gidan iyalan marigayi, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.” Aisha ta rubuta a shafinta na Twitter.

Hakan na faruwa ne har ila yau, a daidai lokacin da gwamnatin ta Najeriya ta ba daukacin sojojin kasar hutun kwana guda, a wani mataki na nuna juyayin rasuwar babban hafsan sojan kasar da wasu sojoji.

“Shugaban kasa ya amince a ba dakarun kasar hutun kwana daya a ranar 24 ga watan Mayu, 2021.” Wata sanarwa dauke da sa hannun Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ta ce

Kazalila, gwamnatin ta ayyana fara zaman makokin kwana uku daga ranar Litinin zuwa Laraba, inda aka ba da umurnin a sassauta tutoci a gine-gine da ma’aikatun gwamnatin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG