Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Sanya Hannu Kan Kasafin Kudin 2023


Shugaban Najeriya yayin da yake sanya hannu kan kasafin kudin 2023 (Facebook/Bashir Ahmad)
Shugaban Najeriya yayin da yake sanya hannu kan kasafin kudin 2023 (Facebook/Bashir Ahmad)

A baya, fadar shugaban kasar ta tsara kasafin kudin na bana akan naira tiriliyan 20.51.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar 2023.

Kasafin kudin na bana, wanda ya samu karin naira tiriliyan 1.32 zai lakume naira tiriliyan 21.83.

A baya, fadar shugaban kasar ta tsara kasafin kudin na bana akan naira tiriliyan 20.51.

Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin ne yayin wani biki da aka yi a fadarsa a ranar Talata a Abuja.

Bikin sanya hannu kan kasafin kudin na bana ya samu halartar shugabannin majalisun dokokin kasar.

A makon da ya gabata majalisar dokokin kasar ta amince da kasafin kudin.

Shugaban na Najeriya wanda ke shirin kammala wa’adin mulkinsa na biyu, ya ce, ya sanya hannu kan kasafin kudin ne don a fara aiwatar da shi ba tare da bata lokaci ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG