Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ne ya bada hujjar da ya sa ba su iya zartar da kasafin kudin shekara 2023 ba. Lawan ya ce kudurin Kasafin Kudin ya zo Majalisar ne da wasu matsaloli da kwamitocin Majalisar dattawa da ta Wakilai suka gano a lokacin da su ke daidaita alkaluman abinda aka yi da kuma abinda aka gabatar wa majalisar. Lawan ya ce matsalolin ba su da sauki a tuntube kuma dole ne kwamitocin su tsaftace lissafin kafin a zartar da kasafin, sai dai bai bada cikakken bayani kan irin matsalolin da aka gano a kasafin ba.
A hirar shi da Muryar Amurka, masanin harkokin siyasa da gudanar da mulki Dokta Abdurahman Abu Hamisu ya ce ruwa ba ya tsami banza domin in ma an taba irin wannan jinkiri a aikin kasafin kudin kasar to zai zama da dadewan gaske.
Hamisu ya ce Majalisar ta jinkirta ne domin a baya ta koka cewa ma'aikatu da hukumomin gwamnati ba su zo kare kasafin kudin su ba. Hamisu ya ce akwai wani abu a kasa da ya sa Majalisar ta yi masu barazana cewa za ta hana su kasafin Kudin idan ba su bayyana a gaban Majalisar ba. Hamisu ya ce ta haka ne Majalisa ke yi wa ma'aikatun barazana domin su samu nasu kason.
A nashi bayanin, shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilai Alhassan Ado Doguwa yana cewa haka siyasa ta gada, dole ne mutane su bayyana ra'ayoyin su,amma gaskiyar al'amari shi ne shugaban kasa ya kawo kasafin kasa, kuma ya kawo kwarya-kwaryar kasafi, saboda haka Majalisa ta ga cewa ya dace ta hada su ga baki daya, saboda ta cika wa al'uman kasa alkawalin da ta yi na kammala Kasafin Kudi a karshen shekara.
A watan Oktoba ne Shugaban Kasa Mohammadu Buhari ya gabatar wa hadaddiyar Majalisar da Kasafin Kudin shekara 2023 na Naira Triliyan 20.5.
Saurari rahoton cikin sauti: