A Yau Litinin Sarauniya Elizabeth ta Birtaniya ke cika shekaru 60 a gadon sarauta.
Ta na ‘yar karamar Gimbiya ta zama sarauniya a ranar 6 ga watan Fabarairun shekarar 1952 bayan rasuwar mahaifin ta sarki George na shida, wanda ya yi jinyar shekara da shekaru.
Wankan sarautar Elizabeth ne irin shi na farkon da aka nuna kai tsaye a talbijin din BBC ga miliyoyin ‘yan kallo, bayan an gama, daga bisani wasu miliyoyin mutane su ka kalla a Amurka da Canada.
Galibi dai, Sarauniya Elizabeth kan yi bikin zagayowar ranar hawanta gadon sarauta, salun alun, ba wata kwaramniya, amma a kan shirya jerin wasu abubuwan da ake yi a duk tsawon shekara.
Sarauniyar da maigidan ta, Yarima Philip, da kuma sauran ‘yan gidan sarautar, na shirin yin rangadi a wasu kasashen da ke karkashin masarautar ta, kasashen su ne Canada da Malaysia da Singapore da kuma Belize.