Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfanin sarrafa takin zamani mafi girma a duniya mallakar kamfanin Dangote.
Kamanin, wanda ke unguwan Lekki a jihar Legas wacce ke kudu maso yammacin Najeriya, zai rika sarrafa takin zamani samfurin Urea da Ammonia.
Ana kuma sa ran zai samar da tan miliyan 3 a shekara domin amfanin ciki da wajen Najeriya.
A jawabinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kamfanin a matsayin abin alfahari wajen ci gaban tattalin arziki da saka jari a kasar.
Ya kuma yi kira ga sauran ‘yan kasuwan Najeriya da su yi koyi da shugaban kamfanin na Aliko Dangote wajen saka jari a cikin gida, domin samar da aikin yi da kuma gina kasa.
Masana tattalin arziki irinsu Dr. Dauda Mohammed Kontagora na cewa hakan zai iya samar da aikin yi da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.
A bangarensa shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya ce wannan kamfani zai samar da ayyukuan yi ga dubban matasan kasar da kuma sarrafa takin zamani domin amfanin manoman ciki da wajen kasar.
Bayan kaddamar da wannan katafaren kanfanin, har ila yau shugaba Buhari ya duba aikin gina sabon tashar jiragen ruwa domin rage cunkoso a tashar jiragen ruwa ta Tincan da Apapa da yanzu haka suka cunkushe kuma suke kawo tsaiko wajen hadahadar kasuwanci zuwa ciki da wajen Najeriya.