Attajirin Najeriya Aliko Dangote shi ne mutum na 117 da ya fi yawan arziki a duniya cikin attajirai 500 da kamfanin Bloomberg mai yin kididdiga ya yi nazari akansu.
Arzikin Dangote ya kai dala biliyan 17.8 a cewar Bloomberg.
Kididdigar wacce aka fitar a ranar Litinin, ta nuna cewa Dangote, wanda ke da kamfanonin siminta, sukari, gishiri, taki da sauran na’ukan abincin sarrafawa, shi ne kadai dan nahiyar Afirka da ya samu shiga jerin attajiran duniya.
Attajirin na Najeriya, wanda dan asalin jihar Kano ne, na fadada harkokin kasuwancinsa zuwa fannin man fetur da sauran dangoginsa.
Kididdigar ta Bloomberg ta kan auna yawan arzikin attajiran duniya 500 ne a kullum inda Dangote inda ta saka Dangote a matsayin 117.
Hakan har ila yau ya kara jaddada matsayin Dangote a zaman attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka.
Elon Musk dan kasar Amurka, shi ne mutumin na farko da ya fi kowa arziki a duniya inda ya mallaki dala biliyan 194.
Ya shahara ne a fannin kere-keren fasahohin zamani kamar yadda kididdigar ta Bloomberg ta nuna.