Yau majalisar zartaswa ta Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta dauki wasu muhimman matakan da zasu kaiga inganta samar da wutar lantarki da samar da wadataccen ruwan sha da na aikin noma.
Bayan taron gwamnati ta bada sanarwar daukan kwararan matakan domin tabbatar da cewa an inganta wutar lantarki, da ruwan sha da ruwan noma ta hanyar inganta madatsun ruwa a kasar.
Kazalika gwamnatin ta dauki matakan inganta tsaro da kare haduran jiragen sama.
Ministan albarkatun ruwa Suleiman Adamu Kazaure ya bayyana matakan da gwamnati za ta dauka.Ya ce kodayake ana samar da wutar lantarki kusan kilowat dubu bakwai amma saboda matasalar layin kebul dubu biyar kawai ake rabawa mutane, ke nan ana hasarar dubu biyu kowace rana kuma dole ne gwamnatin tarayya ta biya kudinsu. Gwamnati zata fito da wani tsari da zai inganta abunda ake ba jama'a ta hanyar kara bada kashi 40 na hannun jarin kamfanonin dake raba wuta yayinda su 'yan kasuwa dake da kashi 60 zasu kara nasu kason.
Ta fuskar ruwan sha zasu inganta madatsun ruwa tare da gina wasu sabbi.
Shi ma Sanata Hadi Sirika ministan sufurin jiragen sama ya bayyana cewa za'a sayi sabuwar naurar dake tantance dalilin hadarin jirgin sama saboda wadda kasar ke anfani da ita tsohuwa ce kuma ta kone.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum