Majalisar zartaswar tarayyar Najeriya ta dauki muhimman matakan da zai kai ga inganta samar da wutar lantarki da kuma samar da wadataccen ruwan sha da na noma.
Bayanda majalisar ta kammala taronta na mako mako karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, gwamnatin ta bada sanarwar cewa zata dauki mataki mai kwarin gaske domin tabbatar da cewa an sami inganci a fannin harkokin tsaro a kasar da kuma kare haduran sufurin sama kamar yadda yake a sauran kasashen duniya.
A fannin samar da wutar lantarki, ministan albarkatun ruwa Suleiman Adamu Kazaure ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya zata fito da wani tsari da za a kara inganta hanyoyin samar da wuta, bisa ga cewarshi, za a duba kamfanonin da ba zasu iya samar da wuta yadda ya kamata ba, sai gwamnati ta nemi hanyar da zata shiga ciki.
A nasa bangaren, ministan harkokin sufurin sama Saneta Hadi Sirika yace gwamnatia zata sayi sabuwar na’urar tantance dalilin hadura irin na zamani domin inganta harkokin sufurin jiragen sama.
Ga dai rahoton da wakilinmu Umar Faruk Musa ya aiko daga Abuja
Facebook Forum