Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Ondo ta sha alwashin samun zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a jihar


Shanun Fulani wurin kiwo da kan jawo rigima tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Shanun Fulani wurin kiwo da kan jawo rigima tsakanin Fulani makiyaya da manoma.

Gwamnatin jihar Ondo tace zata samar da dawamammen zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a jihar

Babban hadimin gwamnan jihar ta Ondo Dr. Abbas Mimiko ne ya bada tabbacin a wajen nadin sarkin hausawan Ore Alhaji Abdullahi Bagobiri a fadar Olore of Ore Oba Johnson Olatunmide.

Gwamna Olusegun Mimiko ta bakin hadinsa yace gwamnatin Ondo tana kokari domin samo masalaha inda makiyayi zai kula da dabbobnsa ba tare da yiwa manoma barna ba saboda jihar Ondo jihar manoma ce.

Oba Olatunmide yace Abdullahi Bagobiri ya zauna lafiya da mutane a garin Ore.

Alhaji Shehu Kazere Bayero hakimin Gwarzo cewa ya yi akwai sakon godiya ga shi mai girma sarkin Ore da kuma fatan za'a samu kyakyawan hadin kai da zaman lafiya tsakanin hausawa da al'ummar yarbawa da suke tare. Ya kira sabon sarkin ya zama mai gaskiya da adalci.

Sarkin hausawan Kogi Baba Sale ya fada cewa ya yi mamakin irin wayan al'umma da ya samu a Ore. Yace bai san akwai hausawa masu dimbin yawa a garin ba. Yana fata za'a samu cigaba.

Sarki Abdullahi Bagobiri yace ranar babbar rana ce a gareshi. Yayi addu'a ala ya mayarda kowa gidansa lafiya. Ya ce zai rike addini da adalci da son al'ummarsa kamar 'ya'yan da ya haifa a cikinsa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG