Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Na Da Koshin Lafiya – Ndume


Shugaba Muhammadu Buhari yayin ziyararsa a Borno (Facebook/Bashir Ahmad).
Shugaba Muhammadu Buhari yayin ziyararsa a Borno (Facebook/Bashir Ahmad).

“Ina ga yanzu ya kamata bangaren ‘yan adawa su sake zama su ga me za su yi magana kuma akai.

Shugaban Kwamitin da ke kula da sha’anin dakarun Najeriya a Majalisar Dattawan kasar, Sanata Ali Ndume, ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari na da koshin lafiya.

Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta kudu a majalisar, ya yi nuni da irin zirga-zirgar da Buhari ya yi ta yi, ba tare da ya nuna ya gaji ba, yayin ziyarar yini daya da ya kai a jihar Borno.

“Ni kaina na gaji, amma shugaban (Buhari) ya yi ta zirga-zirga har tsawon sa’a shida, tun da ya sauka da misalin karfe 10, mun yi ta zagaya wa har zuwa karfe hudu, kafin daga baya ya tafi.” Ndume ya fada a shirin “Politics Today” na gidan talabijin din Channels a ranar Alhamis

“Saboda haka, duk masu cewa shugaban ba shi da lafiya, magana kawai suke yi, domin sai da muka zagaya yankunan jihar hudu baki daya.”

A cewar Ndume, hakan ya nuna cewa Buhari yana da koshin lafiya, “idan aka duba yadda ya yi hira da Arise TV, ya je Legas, ya kuma zo nan Borno.”

“Ina ga yanzu ya kamata bangaren ‘yan adawa su sake zama su ga me za su yi magana kuma akai,” amma ba batun rashin lafiya ba, a cewar Sanatan.

A ‘yan watannin baya an yi ta raderadin shugaban na Najeriya mai shekara 78 ba shi da koshin lafiya, batun da fadarsa ta musanta.

A karshen watan Maris Buhari ya je London don duba lafiyarsa, inda ya kwashe mako biyu a can.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG