Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Najeriya Ya Mutu A Kogin London Yayin Ceto Wata Mata


Kogin Thames da ya ratsa ta birnin London (AP Photo/Frank Augstein)
Kogin Thames da ya ratsa ta birnin London (AP Photo/Frank Augstein)

"Folajimi Olubunmi-Adewale, jarumi ne na kwarai a wannan birni namu, wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin ceto wani ran" Magajin birnin London Sadiq Khan ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Ruwa ya ci wani dan asalin Najeriya mai shekara 20 yayin da yake kokarin ceto wata mata da ta fada Kogin Thames da ya ratsa birnin London a Ingila.

Jaridun Birtaniya da dama sun ruwaito cewa Folajimi Olubunmi-Adewale ya fanjama cikin kogin ne bayan da hango matar ta fada cikinsa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na daren ranar Asabar.

Bayanai sun yi nuni da cewa wani mutum na biyu, wanda shi ma ya ga fadawar matar, ya shiga kogin domin ya ceto ta.

Karin bayani akan: Birtaniya​, Olubunmi-Adewale, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Jami’an ba da agajin gaggawa sun garzaya kogin a lokacin da aka sanar da su, inda daga baya suka ceto matar da wani mutum daban, amma ba su ga Olubunmi-Adewale ba.

Rahotanni sun ce sai da misalin karfe 6 na safe aka ga gawar wani mutum, wacce daga baya aka ayyana a matsayin ta Olubunmi-Adewale ce.

"Folajimi Olubunmi-Adewale ya fi kowa a cikinmu. Jarumi ne na kwarai a wannan birni namu, wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin ceto wani ran. Tunanina da addu'o'ina na tare iyalansa da abokansa a wannan lokaci na alhini." Magajin birnin London Sadiq Khan ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Shaidu sun ce igiyar ruwan kogin na Thames da ke kadawa a lokacin na da karfin gaske, abin da ake ganin ya sa matashin ya gaza cimma burinsa.

Jama’a da dama a kasar ta Birtaniya, sun jijinawa Olubunmi-Adewale bisa wannan namajin yunkuri da ya yi.

Thames, kogi ne da ya ratsa ta yankin kudancin Ingila da ya hada da birnin https://www.voahausa.com/s?k=London&tab=all&pi=1&r=any&pp=10.

Shi ne kogi mafi tsawo a daukacin Ingila kuma na biyu a tsawo a daukacin kasar ta Birtaniya baya ga Kogin Severn da ya kasance na farko.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG