Shugaba Raul Castro na Cuba yace, daidaituwar kawance tsakanin kasarsa da Amurka ba zai tabbata ba sai in har Amurka ta dage musu takunkumin kasuwanci da ta kakabawa masu tare da janye mamayar sansanin sojojin Guantanamo da Amurka ke cigaba da rikewa ba bisa ka’ida ba.
Haka kuma sai ta dakatar da kafarta ta yada labaran radio ko talbijin da ke rarraba kan ‘yan kasarsa. Bugu da kari kuma Amurka ta biya diyya saboda karya tattalin arzikin kasar ta Cuba.
A jawabinsa na farko a taron Majalisar Dinkin Duniya, Shugaba Castro yace, ba za su gushe ba suna mikawa Majalisar daftarin kudurin kalubalantar takunkumin karya tattalin arzikin da Amurka ta kakabawa kasar ba har sai an dage shi.
Shugaban Amurka Barack Obama ya nuna goyon bayan dage takunkumin, amma yace abu ne da yake bukatar yardar ‘yan Majalisun Dokokin Amurka.
Duk da yake dai a makon da ya gabata yace suka yi ta samun tarnaki da Cuba,dangane da maganar mutunta ‘yancin bil’adama.