Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boma Bomai da Harbe Harbe Daga Jirgin Sama a Bajoga da Ashaka


Jirgin Saman Yakin Najeriya.
Jirgin Saman Yakin Najeriya.

A wayewar garin yau Alhamis al’umar garin Bajoga da Ashaka sun tashi cikin wani irin hali na tashin hankali.

A wayewar garin yau Alhamis al’umar garin Bajoga da Ashaka sun tashi cikin wani irin hali na tashin hankali, kasancewar suna tajin harbe harbe daga gabashin garin Bajoga. A cewar wani mazauni garin, harbe harbe ta kota ina da shawagin jirage da tashin boma bomai tunda garin Allah ya waye su ke taji.

Mutane da dama basu samu damar fita ba don al’amurransu na yau da kullun ba. Wadannan harbe harben da tashin boma bomai sun fara ne tun da kamar karfe 7:00 na safe har zuwa karfe 2:00 na rana, mutane basu samu fita ba.

A cewar wani ma zauni garin yace labari ya samesu da cewar ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun je wasu anguwanni sunga mutane suna kokarin guduwa amma sun ce musu kada su gudu, don ba sunzo don nema kowa bane illa sunzo neman jami’an gwamnati ne.

Boma Bomai da Harbe Harbe Daga Jirgin Sama a Bajoga da Ashaka - 4'13"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG