Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom Ya Tashi a Tashar Bauchi Dake Garin Gombe


 Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko-Haram.
Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko-Haram.

Rahotanni daga jihohin Bauchi da Gombe na cewa an ga 'yan bindiga cikin motoci suna ratsa wasu garuruwa a jihar Bauchi da Gombe

'Yan bindigan basu harbi kowa ba to saidai da alamun yunwa ta galabaitasu. Wai suna gararamba ne a cikin daji.

To amma an bada labarin cewa bom ya tashi a tashar mota da ake kira tashar Bauchi a garin Gombe. Shaidun gani da ido sun ce akalla mutane biyar sun mutu yayinda wasu masu yawa sun samu rauni.

An ce wata mata ce ta zo wai zata yi tafiya. Ta biya kudin mota sai ta saka jakarta cikin motar amma ta fita ta koma gefe daya tana waya sai bom ya tashi a motar. Lamarin ya faru ne wajejen karfe takwas na yamma. Jami'an tsaro basu isa wurin ba da wuri.

Wani jami'in tsaro ya ga matar lokacin da take waya ya kira wani yaro yace a binciketa amma yaron yace fasinja ce babu damuwa. To yaron yana cikin wadanda suka rasa rayukansu. Ita dai matar ba'a samu an kamata b. Ta arce.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG