Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya dauki alhakin harin kwantan baunar da aka kaiwa wani jerin gwanon motoci da jami’an tsaro ke jagoranta, akan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, inda kuma ya yi ikrarin cewa sun sace wasu yan sanda mata guda 11 batun da ‘yan sanda ke musantawa.
Kan wannan batu ne Wakilin Muryar Amurka a Abuja, Hassan Maina Kaina, ya tuntubi hedikwatar yan sandan Najeriya domin tabbatar da gaskiyar wannan batu, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Borno, Mista Damian Chukwu, wanda kuma ya musanta maganar yace shi dai yana da masaniyar an kashe jami’arsu guda daya.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa tabbas anyi wa jerin gwanon kwantan bauna inda aka harbi direban da ke tuka motar da marigayiyar ke ciki a bayansa, ya kuma lallaba ya tsere, haka kuma an harbi wani sajan dake jagorancin tawagar wanda shima ya mutu kuma sun ‘dauke bindigarsa. Sai kuma wani ‘dan sanda dake dauke da barkonan tsohuwa har yanzu ba a ganshi ba.
Domin karin bayani saurari hirar Hassan Maina Kaina da kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno Mista Damian Chukwu.
Facebook Forum