Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadin Kan Duniya Na Da Muhimmanci Wajen Samun Ci Gaba Mai Dorewa - Tinubu


SHugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu a Hadaddiyar Daular Larabawa
SHugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu a Hadaddiyar Daular Larabawa

Shugaban ya ayyana cewa babu wata kasa da za ta cimma muradan ci gaba mai dorewa ita kadai, inda ya jaddada cewa hadin gwiwar duniya na bukatar yin aiki tare da musayar ilimi da kuma tallafawa juna.

A ranar Laraba a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa, Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya baiwa al’ummar duniya tabbacin cewa a shirye Najeriya take tayi aiki tare da sauran kasashe wajen gina jajirtacciyar duniya mai cike da adalci da cigaba mai dorewa ga kowa.

Shugaba Tinubu ya gabatar da jawabi a rana ta biyu ta taron makon ci gaba mai dorewa na Abu Dhabi na bana.

Shugaban ya ayyana cewa babu wata kasa da za ta cimma muradan ci gaba mai dorewa ita kadai, inda ya jaddada cewa hadin gwiwar duniya na bukatar yin aiki tare da musayar ilimi da kuma tallafawa juna.

“Yaki da sauyin yanayi bai takaita ga wajibai akan muhalli ba illa dama ce ga tattalin arzikin duniya ya sauya makomar nahiyarmu dama kasuwar makamashi ta duniya.

“A matsayinmu na shugabanni kuma masu ruwa da tsaki dake rayuwa a wannan duniya, muna tsaye ne a wata mahada mai mahimmancin gaske ga tarihin dan adam. Domin samun nasara, wajibi ne mu zama masu fikira da hadin kai da daukar kwararan matakan gaggawa a matsayinmu na al’ummar duniya daya,” a cewar Tinubu.

Shugaban ya kara da cewa mahalarta taron sun jajirce duk da suka da s uke sha a wurin masu fafuftikar ganin cewa an kiyaye muhalli domin ci gaban al’umma da ma manazarta a cikin lokaci kadan.

Ya kuma umarci jami’an gwamnatinsa da cikin tawagar da ta biyo shi taron da su tabbatar sun aiwatar da manufofin gwamnatinsa a da zaran sun isa gida bayan taron da ke tafiye a Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular larabawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG