Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korafin Wasu Tsofaffin Sojojin Najeriya Kan Yadda Suka Bautawa Kasa


Bikin Ranar Tunawa Da Mazan Jiya
Bikin Ranar Tunawa Da Mazan Jiya

An samu salwantar dubban daruruwan rayukkan jama'a a Najeriya, da suka hada da shugabanni da manya da kananan jami'an soji sakamakon juyin mulki na farko har zuwa yakin basasa da aka yi tun shekaru 1966-70

Wannan ne ya sa ake gudanar da bukukuwan tunawa da mazan jiya wadanda suka sadukar da rayukansu wajen kare martabar kasar, .

Sai dai wasu daga cikin tsofaffin sojoji da ke raye a yanzu sun ce, Najeriya ba ta nuna gamsuwa da sadaukar da rayukan su da suka yi ba.

Ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966 aka yi juyin mulki na farko a Najeriya aka hambarar da jagororin jamhuriya ta daya, wanda ya yi sanadin salwantar rayukkan manyan mutane da suka hada da Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa, Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Firimiyan kudu Samuel Ladoke Akintola da Ministan Kudi Festus Okotie-Eboh.

Haka ma an samu salwantar rayukan manya da kananan sojjoi da suka hada da Birgediya Zakari Maimalari, Birgediya Samuel Ademulegun, Kanal Kur Mohammed da dai sauransu.

Farfesa Abubakar Abdullahi na sashen nazarin kimiyar siyasa a Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ya ce wannan juyin mulki ya haifar da matsaloli masu tarin yawa.

Sigar da wannan juyin mulkin ya dauka a cewar masana tarihin da kimiya siyasar Najeriya ya yi tasiri wajen shugabanci da zamantakewar jama'ar da ke Najeriya a wannan lokacin.

Yakin basasa da ya biyo baya, ya gudana tsakanin shekarun 1967 zuwa Janairun 1970, ya yi sanadin salwantar rayukan dubban daruruwan jama'a hadi da jami'an soji.

Bisa ga rayukan mazan jiya da aka rasa ya sa gwamnatin Najeriya ta tsayar da ranar 15 ga watan Janairu na kowace shekara a zaman ranar tunawa da 'yan mazan jiya wadanda suka sadukar da rayukansu wajen kare maratbar Najeriya.

Wannan kuma bai tsayu kan wadanda suka yi yakin basasa ba kadai ya kunshi dukan jami'an da suka fafata domin kare martabar Najeriya a wurare daban daban, to sai dai wasu daga cikin tsofaffin jami'an soji sun ce ya kamata a kula da su fiye da yadda suke samu yanzu.

Shugaban kungiya tsofaffin sojoji ta Najeriya reshen jihar Sakkwato Copral Aliyu Abdullahi Danchadi ya ce da gwamnatin Najeriya ta gamsu da yadda suka sadaukar da rayukansu a kasa, da ba za ta hana su hakkokinsu sai sun yi zanga-zanga ba.

Sakataren kula da yada labarai na kungiyar Sergent Sagir Gambo Ruma yace yanayin da tsafaffin soji suke ciki yanzu a Najeriya sai dai ace Alhamdulillahi.

Kowace shekara a kan yi gidauniya domin tallafawa 'yan mazan jiyan da ke raye da kuma iyalan wadanda suka rasu, amma kuma duk da haka suna bukace da samun kulawa wadda ta fi wannan.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Korafin Wasu Tsofaffin Sojojin Najeriya Kan Yadda Suka Bautawa Kasa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:03 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG