Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zan Lamunci Gazawar Kwamandojinmu Ba – Farouk Yahaya

Manyan sojojin Najeriya yayin wani taron karara juna sani (Facebook/Dakarun Najeriya).
Manyan sojojin Najeriya yayin wani taron karara juna sani (Facebook/Dakarun Najeriya).

“Ina sane da cewa akwai matsalolin da ke shafar ayyukan da muke yi a sassan kasar nan, amma ina muku albishir da cewa, ana kan daukan matakan da za su kawo karshen wadannan kalubale.”

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar-Janar Yahaya, ya ja kunnen kwamandojinsa da ke filin daga inda ya ce ba zai amince da gazawarsu ba a yakin da suke yi da masu ta da zaune tsaye a sassan kasar.

Laftanar-Janar Yahaya ya bayyana hakan ne yayin bude taron zango-zango na shekara da ake yi wanda ya gudana a Abuja.

Yayin jawabin nasa, babban hafsan sojin kasar ya yi kira ga kwamandojin da su zage dantse wajen kirkirar dabarun da za su shawo kan matsalar tsaron da ke addabar Najeriya.

“Ba zan lamunci gazawa ba kowacce iri ce.” Laftanar-Janar Yahaya ya ce, kamar yadda wata sanarwar rundunar dakarun Najeriyar ta fitar ta ce.

Laftanar-Janar Yahaya (tsakiya) (Facebook/Dakarun Najeriya)
Laftanar-Janar Yahaya (tsakiya) (Facebook/Dakarun Najeriya)

“Ina sane da cewa akwai matsalolin da ke shafar ayyukan da muke yi a sassan kasar nan, amma ina muku albishir da cewa, ana kan daukan matakan da za su kawo karshen wadannan kalubale.”

A farkon jawabinsa, Laftanar-Janar Yahaya ya ce ya karbi ragamar tafiyar da rundunar sojjin Najeriya a wani “matsanancin lokaci da Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro mai cike da sarkakiya.”

Babban Hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar-Janar Farouk Yahaya (Facebook/Dakarun Najeriya)
Babban Hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar-Janar Farouk Yahaya (Facebook/Dakarun Najeriya)

“Amma ina so na nanata cewa, rundunar sojin Najeriya karkashin jagorancina, zai ci gaba da kara kaimi da daukan matakan da za su kawo karshen matsalolin tsaro.”

Najeriya na fuskantar matsalar ‘yan bindiga a arewa maso yammacin, arewa maso tsakiya da kuma kalubalen ‘yan Boko Haram da ISWAP a arewa maso gabashi, sai kuma ‘yan aware a kudu maso gabashi.

XS
SM
MD
LG