Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Kan Matar Da Aka Hallaka Da Wuka A Birnin Landan


Matar nan da aka kashe ta hanyar caka mata wuka a kan titin birnin London, matar wani Farfesa ce na jami’ar jihar Florida dake nan Amurka.

Darlene Horton, mai shekaru 64, ta rasa ranta sakamakon hari da wani matashi ‘dan asalin Somalia ya kai hari da wuka Dandalin Russell, dake matattarar ‘dalibai da ‘yan yawon bude ido.

A jiya Alhamis ne ‘yan sandan London suka ce basu sami wata hujja da ke nuna alamun aikin ta’addanci a harin ba, da ya kuma raunata wasu mutane biyar, wanda biyu daga cikin su ‘yan kasar Australia ne, ‘daya Isra’ila, da ‘dan Amurka da kuma dan asalin Birtaniya, baki ‘dayansu dai babu wanda yake cikin mawuyacin hali.

Amma, ‘yan sanda sun ce ta yiwu harin na da nasaba da matsalar tabin hankali.

‘Yan sanda sun kame matashin dan shekaru 19 da haihuwa a filin Russell dake kusa da jami’ar London bayan da suka yi amfani da wata na’urar kashe jiki. Matashin da ba a kai ga bayyana sunansa ba yana hannun ‘yan sanda yanzu haka a wani asibiti dake birnin na London.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya bayyana harin a matsayin wani mummunan aiki, kuma yace yana jajantawa mutanen da harin ya shafa.

Wannan hari faru ne a dai dai ranar da jami’an London suka fitar da sanarwar ‘kara ‘yan sandan sintiri a birnin, a kokarin kare hare haren ayyukan ta’addanci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG