Wata sanarwa daga birnin Rabat tace sarki Phillippe na Belgium yayi kira ga sarki Mohammed na neman hadin kai sosai a ci gaba da farautar Salah Abdelsalam, wanda har yanzu yake buya tun bayan da ya tsallaka zuwa Belgium daga Faransa sa'o'i bayan da aka kai hare hare a birnin Paris ranar 13 ga watan nan.
Makon jiya Morocco ta baiwa 'Yansandan Faransa bayanai da suka kai hukumomin kasar ga kashe Abdelhamid Abaaoud wanda ake zargi shine ya kitsa hare haren na Paris, bayanda aka gano shi a wani daki a arewacin birnin Paris,ranar 18 ga wannan wata.
Ahalinda ake ciki kuma Amurka ta lashi takobi zata yi aiki da kawayenta wajen murlkushe kungiyar ISIS, bayan jerin hare hare da kungyar ta kai a kasashen waje, inda bata da iko kamar Syria da Iraqi.
Kamar yadda jami'an Amurka suka bayyana, mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ne ya gabatar da wannan sako ga wakilan kasashe da suke cikin rundunar taron dangi a fadin duniya da zummar ganin bayan ISIS, a taro da suka yi ta fuskar difilomasiyya a ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka jiya Litinin.