Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Almundahana A Wasu Kananan Hukumomin Nijar


Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani

Birane kamar su Abala Tanout Tahoua Zinder da Yamai na daga cikin irin wadanan wurare da sufetoci masu aikin bincike suka gano an handame daruruwan million cfa kamar yadda ministan cikin gidan Nijar Janar Mohamed Toumba ya bayyana

Wani bincike a ofisoshin magaddan gari da na shuwagabanin rusassun majalissun jihohi a Nijar ya bankado wawurar makuddan miliyoyin CFA, lamarin da ya sa gwamnatin mulkin sojan kasar ta fara yunkurin damka batun a hannun hukumar yaki da cin hanci don ganin mutanen da ake zargi da hannu a wannan almundahana sun gurfana.

Birane kamar su Abala, Tanout, Tahoua, Zinder da Yamai na daga cikin irin wadanan wurare da sufetoci masu aikin bincike suka gano an handame daruruwan milliyoyin cfa, kamar yadda ministan cikin gidan Nijar Janar Mohamed Toumba ya bayyana.

Ya kuma zayyana wasu daga cikin da’irorin da ake zargin an tafka irin wannan alumndahana.

Ya ce a da’irar Ourafan miliyan 169 na cfa aka gano an salwanta, miliyan 287 a Oualalewa sai Zinder mai miliyan 355 da Tahoua mai miliyan 244.

Wasu ‘yan kasa da muka nemi jin ra’ayoyinsu sun yi na’am da matakin na gwamnati.

Tuni aka damka wa hukumar yaki da cin hanci COLDEFF rahotannin illahirin wuraren da aka riga aka kammala bincike a yayinda ake jiran jami’ai su karkare binciken dake gudana a sauran yankunan domin damka komai a hannun hukumar ta COLDEFF wacce za ta bi hanyoyin tatso kudaden da aka wawure inji ministan.

Shugaban kawancen kungiyoyin yaki da cin hanci RNAC Omar Adamou ya yaba da wannan kudiri, koda yake a cewarsa akwai bukatar gyara.

A watan Afrilun 2024 ne shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamne Tiani ya rusa majalisun kananan hukumomi da na jihohi watanni 9 kenan bayan juyin mulkin da ya jagoranta.

Ko a zamanin mulkin farar hula dangantaka kan yi tsami a tsakanin irin wadanan wakilai da hukumomin kolin kasa sakamakon zargin wasu daga cikinsu da rubda ciki kan kudade ko karkatar akalar tallafin cimakar da gwamnatin tsakiya ke aikewa domin talakawa, koda yake wasunsu na danganta wannan rashin jittuwa da dalilan siyasa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Bayan Bincike An Gano Almundahana A Wasu Kananan Hukumomin Nijar .MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG