Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Shin Ya Kamata A Daina Sa Bayanin Addini Da Asalin Inda Mutum Ya Fito A Takardar Neman Aiki Ta CV?


Wasu matasa da masana kundin tsarin mulki na ganin cewa ya dace a cire bayanin addinni da asalin jihar da mutum ya fito a takardar bayanin mai neman aiki wato CV don rage matsalolin kabilanci a kasar.

ABUJA, NIGERIA- A daidai lokacin da ake neman hanyoyin samar wa matasa masu zaman kashe wando ayyukan yi da kuma warware rikice-rikice masu nasaba da kabilanci da banbance-banbancen addini da wasu lokutan a ke nunawa a fannin daukan aiki a Najeriya,

Matasa ‘yan Najeriya sun fara yin kiraye-kirayen a daina sa bayanin asalin jihar da mutum ya fito da kuma addininsa a takardar bayanin mai neman aiki wato CV ne a kafaffen sada zumunta inda su ke cewa hakan zai taimaka wajen ba wa wadanda suka kware aiki ba tare da la’akari da addininsu da inda suka fito ba, baya ga rage matsalolin da suka shafi kabilanci da nuna banbancin addinin wajen daukan aiki.

Ko menene kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar a game da wannan batun, fitaccen lauya barrister Mainasara Kogo ya ce maganar CV ya na da amfani idan za abi adalci da gaskiya a cikin kasa, wato ma’ana idan za abi wani tsarin mulkin kundin kasa da ya ce ayi daidaito wajen duba halaye masu kyau, amma idan hakan zai kawo rashin bin adalci to za a saba ga wani fannen tsarin mulkin kundin kasar.

Tun ba yau ba ake fama da matsalolin da suka shafi rashin yin daidaito wajen daukan aiki a ma’akatun gwamnati da ma kamfanoni masu zaman kansu kuma a wasu lokutan ake danganta kin daukan mutum aiki ga kiyayya ga asalin shiyyar da ya fito ko banbancin addini da dai sauransu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:

Shin Ya Kamata A Daina Sa Bayanin Addini Da Asalin Inda Mutum Ya Fito A CV
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG