Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bauchi: Jam’iyyu 25 Ke Goyon Bayan APC A Zaben Cike Gurbin Sanatan Da Ya Rasu


Gangamin siyasa a Bauchi
Gangamin siyasa a Bauchi

Gabanin zaben cike gurbin kujerar Sanata Ali Wakili da ya rasu, jam’iyyu 25 sun yi hadakar marawa jam’iyyar APC baya yayinda Dr Ladan Salihu na PDP da Malam Isa Yuguda na GNP na cikin takarar ta wannan Asabar mai zuwa

A jawabin da ya yiwa taron manema labaru, jagoran hadakar jam’iyyun Abdullahi Muhammad, shugaban jam’iyyar APA a jihar Bauchi ya bayyana dalilansu na marawa jam’iyyar APC baya.

Yace idan suna son a samu ci gaba a Bauchi su jam’iyyun sun fito su shaidawa duniya cewa wajibi ne su goyi bayan APC a zaben cike gurbin sanatan da ya rasu saboda yin la’akari da mahimman aikin da APC ta keyi a jihar da tarayya.

Shugaban jam’iyyar NCP dake cikin hadakar Usman Balbaya ya ce akan wannan zaben cike gurbi ne kawai suke marawa APC baya ba zaben shekarar 2019 ba.

Shi kuwa dan takarar jam’iyyar PDP Dr. Ladan Salihu yace babu fargaba koda jam’iyyun hadakar sun kai guda dari. Ya ce baya fargaba saboda mulki daga Allah yake.

A nasa bahasin dan takarar jam’iyyar GPN kuma tsohon gwamnan jihar Isa Yuguda, Malam Isa Yuguda, ya ce ga wanda ya yadda da Allah babu wata fargaba. Duk abun da Allah ya shirya zai yi, zai yi.

A saurari rahoton Abdulwahab Muhammad

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG