Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazabar Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Ta Yi Masa Kashedi Akan Yunkurin Tsige Shugaban Kasa


Yakubu Dogara kakakin majalisar wakilan Najeriya
Yakubu Dogara kakakin majalisar wakilan Najeriya

Shugabannin APC a mazabar kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara da suka hada da kananan hukumomin Tafawa Balewa, Bogor da Dass sun mikawa ofishin jam’iyyar na jiha dake Bauchi wasikar yiwa kakakin kashedi akan yunkurin tsige shugaban kasa

Shugabannin APC da suka fito daga mazabar kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara sun mika wasikar kokensu ga ofishin jam’iyyar dake Bauchi dake dauke da sa hannun mutane 18.

Muhammad Hassan mukaddashin shugaban jam’iyyar na jihar Bauchi ya shaidawa Muryar Amurka cewa wakilan mazabar Yakubu Dogara sun kawo korafi ne akan abun da yace su ma ya damesu. Sun kawo rashin amincewarsu ne ga yunkurin majalisun Najeriya biyu na neman tsige shugaban kasa.

Mutanen mazabar na kananan hukumomin Dass, Bogoro da Tafawa Balewa sun bukaci Yakubu Dogara ya cire hannunsa daga duk abun da ya shafi takun saka tsakanin shugaban kasa da ‘yan majalisa. Idan kuma ya ki su mutanen nasa suna da matakin da zasu dauka a kansa.

Amma wasu hadiman kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, su gana da manema labarai domin bada tasu bahasin. Dar Abdu Gani Bogoro yace tun kafin a yi zabe Yakubu Dogara ne wakilin Shugaba Buhari a Lagos. Baicin haka lokacin da shugaban kasa bashi da lafiya Yakubu Dogara ya tabbata ba’a taba kujerarsa ba. Ya kara da cewa lokacin neman zabe Yakubu Dogara yana shiga mijami’u yana kemfen cewa duk wanda ba zai zabi Buhari ba kada ya zabeshi. Dr Bogoro y ace tsakanin Buhari da Dogara kamar Danjuma da Dan Jummai ne.

Shima Iliyasu Ibrahim Zor yace shi ne yake tallafawa Yakubu Dogara akan harkokin majalisun jihohi da kananan hukumomi. A cewarsa irin maganganun dake fitowa basu da tushe saboda shi ya san babu yadda za’a hada baki da Yakubu Dogara domin a ci mutuncin shugaban kasa. Yace batanci ne ba wani abu ba.

Abdulwahab Muhammad nada karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG