Mayakan Boko Haram su sama da 1600 da zasu gurfana gaban shari’a yau Litinin sun hada da manyan kwamandojin kungiyar da suka tabka aika-aika a Najeriya da wasu kasashen yankin tafkin Chadi irinsu Kamaru da Chadi da Jumhuriyar Nijar.
To saidai tunda akwai wasu kasashe da ka iya neman yi masu nasu hukumci, shin ko yi masu shari’a a Najeriya ya wadatar? Wakilinmu Hassan Maina Kaina ya ji ta bakin masana akan wannan tambaya.
Farfesa Muhammad Tukur Baba na Jami’ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto yace ko da Najeriya ta yanke masu hukunci, ita ma Kamaru zata iya nemansu. Haka ma Nijar ko Chadi. To amma idan akwai yarjejeniya tsakanin kasashen da Najeriya tana yiwuwa a kaisu kasashen, su fuskanci shari’a sai dai in Najeriya tayi masu hukuncin kisa.
Sai dai lauyan tsarin mulki, Barrister Modibo Bakari yace dokar yaki da ta’addanci ta Najeriya bata birgeshi ba saboda bata yi wani tanadin kirki ba kan laifukan da aka kama su a kai. Ya bukaci a yiwa dokokin kasar gyaran fuska.
Shi kuwa Dr Saleh Abba, wani mai fafutikan tallafawa mutanen da ‘yan kungiyar Boko Haram suka daidaita, yana ganin yiwa ‘yan Boko Haram shari’a ba tare da kama masu mara masu baya ba tamkar an kashe maciji ne ba tare da an sare kansa ba.
Ga rahoton Hassana Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum