Kamar yadda alkalumman hukumomin agaji ke bayyanawa, kawo yanzu akwai sama da Fulani makiyaya dubu 17 dake gudun hijira a kasashen Najeriya da Kamaru.
To sai dai yayin da shugabanin wadannan al’ummomi ke kokawa, gwamnatin jihar Taraba dake arewa-maso-gabashin Naijeriya wacce kuma ke makwaptaka da kasar ta Kamaru, tace tana iya bakin kokarinta domin ganin cewa kowa ya koma gidansa tunda hankula sun kwanta.
Hassan Mijinyawa dake zama jami’in yada labaran gwamnatin jihar Taraban, ya ce tuni gwamnan jihar, Arch. Darius Dickson Isiyaku, ya tura mataimakinsa Haruna Manu domin ya je ya tattauna da wadanda suka ficen.
Dangane da wannan al’amarin ne, a kwanaki shaharraren dan kasuwan nan na Afrika, Aliko Dangote, ya bada gudummawar Naira miliyan hamsin (N50m), domin agazawa wadanda lamarin ya shafa.
To amma Barrister Bashir Muhammad, dan majalisar dokokin jihar dake wakiltar mazabar Nguroje, daya daga cikin yankunan da rikicin ya shafa, yace kawo yanzu su basu ga koda kwandala ba.
Ya zuwa wannan lokaci akasarin al’ummomin na gudun hijira ne a garuruwan da suka hada da Maisamari, Ngoroje, Gembu, Baruwa da Jalingo, yayin da wasu kuma suka ketara zuwa Banyo da Sambo Labo da ke jamhuriyar Kamaru.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum