Wasu kungiyoyin matasa dake neman zaman lafiya a Jihar Borno sun kira gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen dakile yawan hare-haren da ‘yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa cikin jihar Borno.
Kungiyoyin su 72 sun yi kiran ne a lokacin wani taron gangami da suka shirya cikin garin Maiduguri, inda suka yaba da aikin da sojojin Najeriya ke yi amma suka nuna cewa har yanzu ana samun hare-hare irin na sari ka noke nan da can musamman a bayan gari.
Alhaji Babagana Gambo, shugaban hadakar kungiyoyin, ya shaidawa wakilinmu Haruna Dauda cewa sunyi kiran ne ganin cewa duk da yakin da ake yi da kungiyar, hare-haren sun ki karewa.
A bangaren mata kuma, Hajiya Yagana Alkali, shugabar matan, tace rikicin ya fi shafar mata, inda take nuni da mata da yawa da aka kashe mazajensu, wadanda ke cikin kunci saboda an barsu da yara. Akwai kuma yara da dama da basu iya ci gaba da makaranta. ‘Yan mata kuma da suka balaga wasu na yin lalata dasu yayinda suka fita daga sansanin ‘yan gudun hijira domin neman abun da zasu ci.
A cewar Hajiya Yagana, mata fiye da dubu arba’in ne yanzu suka rasa mazajensu sakamakon rikicin Boko Haram kana ‘yan mata kimanin dubu biyar ne suka yi ciki.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum