Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan jihar Taraba ya lashi takobin sa kafar wando daya da masu tada hankali


Wurin da aka kai hari a Taraba
Wurin da aka kai hari a Taraba

Yawan tashin hankali a jihar Taraba na mayarda hannun agogo baya lamarin da ya sa gwamnan jihar Darius Isyaku yace dole ne jama'ar jihar su kai zuciya nesa

Bayan rikicin yankin Wukari da Ibi kwana kwanan nan ma an samu tashin hankali tsakanin kabilun Lau inda rayuka suka salwanta.

Amma gwamnan jihar ya lashi takobin sa kafar wando daya da duk wani da ya sake tada hankali a jihar.

Gwamnan ya kira mutane su daina rigima a jihar. Ya sha alwashin kawo karshen tashin tashinar da suke son zama ruwan dare a jihar. Duk wanda ya ki zaman lafiya gwamnan yace zasu taka shi.

Dangane da yadda za'a samu zaman lafiya a jihar shugabannin addini a jihar sun ayyana tattaunawa a wata hanyar da zata tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Imam Abulmummuni Nda babban limamin masallacin Juma'a na Lankabiri yace a fadakar da jama'a cewa Allah ya halarci mutane domin su san juna su kuma zauna tare. Shi ya halirci musulmi da wanda ba musulmi ba.

Shi ma babban mai bishara na Cocin LCCN Rebaran Hanani Ayuba yace akwai bukatar musulmi da kirista su bi koyin littafansu domin magance kaucewa hanya da kuma samun zaman lafiya.

Shugabannin sun bukaci gwamnatin jihar ta yiwa al'ummar jihar adalci ba tare da nuna banbancin addini ko kabilanci ba. Sun kira gwamnati ta samar ma matasa aikin yi domin kada su shiga hannun miyagun mutane.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG