Kalaman na Laporta sun biyo bayan bullar labarin biyan Jose Maria Enriquez Negreira, tsohon mataimakin shugaban kwamitin alkalan wasa wasu kudade.
Barcelona ta biya kamfanin Negreira kusan Yuro miliyan 7 tsakanin shekarar 2001 da 2018.
Biyan kudi da aka yi tsakanin 2016 da 2018 da jimlarsa ya kai miliyan €1.4M, ya sa ofishin haraji na binciken kudaden shiga na kamfanin na Negreira.
Da farko Laporta ya yi ikirarin cewa wadannan kudaden da aka biya, na "wani aikin samar da bayanai ne da aka yi kan alkalan wasa."
A ranar Talata, ya sake nanata cewa Barcelona ba ta biya kudi don wani abu kuma ba.
“Za mu kira taron manema labarai a kai nan bada jimawa ba. Amma Barca ba ta taba sayen alkalan wasa ko alfarma ba. Wannan bai taba zama niyyarmu ba kuma dole a yi bayani dalla dalla. Bayanan gaskiya sun ci karo da na wadanda ke kokarin bayar da wani labari na daban,” in ji Laporta.