Mukaddashin mai hulda na jama'a jam'iyyar PDP ya raftafawa wata sanarwa hannu cewa jam'iyyar bata da wani fargaba domin ragista da a ka yiwa APC. Jam'iyyar PDP tana tinkaho da cewa tana da dimbin miliyoyin 'ya'yanta a duk fadin kasar. Ta dalilin haka zata ci zabe ta kuma cigaba da rike madafin ikon kasar Najeriya. Sai dai a zahirin gaskiya masu kula da harkokin siyasa sun ce cikin PDP ya duri ruwa domin bata yi tsammanin APC zata samu rajista ba kamar yadda Buhari Bello Jega masanin kimiyar siyasa dake aiki a Jami'ar Abuja ya fada. Ya ce hakika abun da ya faru zai iya kawowa jam'iyya mai ci yanzu barazana domin tamkar zai kawo canji ne. Shigowar APC in ji Bello Buhari Jeja wata tafiya ce da ta baiwa mutane daman zabi tsakanin mutane biyu.
Sai dai da yake mayarda martani mai baiwa shugaban PDP shawara Sanata Abubakar Gada ya ce sam, jam'iyyarsa ta PDP bata firgita ba. Ya ce ai ita APC yanzu a ka haifeta. Bata ma fara rarrafe ba balantana tafiya. Sai dai nan gaba tana iya mikewa.Wasu kuma 'yan PDP sun ce Buhari ne kawai idon gari a gamayyar da wasu ke son hawar doronsa su ci moriyar ganga. Ado Bunuyadi nada irin wannan ra'ayin. Ya ce ai Buhari da yana cikin ANPP ya barta ya kafa CPC. To yanzu sun kashe jam'iyyunsu sun hade da shi. Zasu yi anfani da shi su zama abun da suka zama kana su yi watsi da shi kamar yadda suka yi masa a baya. Ya ce ba Buharin suke kauna ba illa wannan rigar mutunci kadan da yake da ita. Itace suke son su fake da ita. Su buya da ita su cigaba da yiwa mutanen Najeriya da'adi.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada rahoto.