Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Ruwan Bama-Bamai A Birnin Khartoum Na Sudan


SUDAN-POLITICS/
SUDAN-POLITICS/

An yi ruwan bama-bamai da jiragen sama a wasu sassan babban birnin Sudan jiya Lahadi, ba tare da nuna alamun cewa bangarorin da ke fada da juna sun shirya ja da baya a rikicin da aka shafe wata guda ana yi, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Duk da tattaunawar neman tsagaita wuta a Saudiyya, birnin Khartoum da garuruwan Bahri da Omdurman da ke makwabtaka da rassan kogin Nilu, sun kasance manyan wuraren da ake gwabza fada tare da yammacin lardin Darfur, tun bayan da sojoji da dakarun sa kai suka fara fafatawa a ranar 15 ga Afrilu.

Bam ya tashi a garin Bahri, sannan an kai hari ta sama a Omdurman da sanyin safiyar Lahadi, kamar yadda wani dan jarida na Reuters da shaidu suka bayyana.

Wani mazaunin kusa da filin jirgin sama na Khartoum, wanda aka rufe tun farkon rikicin, ya ce an yi ta gwabza kazamin fada a tsawon yinin.

Jiya Lahadi Majalisar Dinkin Duniya ta ce tashe-tashen hankulan sun yi sanadin mutuwar akalla mutane 676, tare da raunata 5,576, kodayake ma an samu rahoton bacewar mutane da dama da kuma gawarwakin da ba a binne ba, ana ganin adadin zai fi haka.

Kimanin mutane 200,000 ne suka tsere zuwa kasashe makwabta sannan sama da 700,000 suka rasa matsugunansu a cikin kasar Sudan, lamarin da ya haifar da matsalar jin kai da ke barazanar shigar kasashen ketare don gudun dagula zaman lafiya a yankin.

XS
SM
MD
LG