Jam'iya mai mulki ta kasar Africa ta Kudu tana taron ta na zaben sabon shugaba a daidai lokacin da jami'yar ke fuskantar rarrabuwar kawuna.
Nan da ‘yan kwanaki, wakilai 5,000 za su zabi wani sabon shugaban jam'iyar African National Congress, ANC da zaran jami'yar ta yi wannan zaben.
Ana sa ran zaben zai kawo karshen mulkin shugaban kasar Jacob Zuma wanda ke cike da cece-ku-ce.
Wasu na ganin da zaran an yi wannan zaben, za a kulle babin shugaba Zuma wanda batun cin hanci da rashawar da ake zargin sa da shi ya jefa jam'iyar cikin damuwa.
Wanda duk ya maye gurbinsa a matsayin shugaban jam'iya ana sa ran ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyar a zaben da za a gudanar a kasar a shekarar 2019.
Amma kuma fa shugaba Zuma na iya ci gaba da zamowa shugaban kasa ko bayan zaben sabbin shugabannin.
Sai dai masu kula da harkoki siyasar kasar na cewa ‘yan jam'iyarsa za su shawo kansa da ya yi hakuri ya sauka daga shugabancin jam'iyar kafin zaben.
Facebook Forum