WASHINGTON D.C —
A yau shirin Bana bakwai ya kai ziyara jahar Kaduna da kuma Bauchin Najeriya sa'an nan muka leka jaharKano inda muka ji sababbin kalmomi ko salon magana da matasa kan yi anfani da su a tsakanin su ba tare da bako ya gane abin da suke nufi ba.
A jahar Bauchi, Mohammed Shaffi'u ya bayyana irin tasu kalmar inda ya ce "yau naga wata hanu". wannan yana nufin ya ga wata budurwa ke nan.
Aminu Isah daga Kaduna kuma ya ce "ba yawa bane" wannan na nufin lamarin yayi dai dai.
Saurari cikakken shirin a nan.