A wani koke da wasu daga cikinsu suka yiwa Sashen Hausa na Muryar Amurka, sun bayyana cewa samun aikin yi ya zama dan sarki, ta inda har sai sun bada cin hanci da sadaukar da albashinsu na farko har zuwa na biyu.
“Matsalar da muke fuskanta guda daya ce, lokacin da muke zuwa neman aikin nan, aka ce mu je mu samu wani mutum da yake a Challawa, sunansa Sunday. Da muke je muka same shi, yace sai mun bashi wani abu” a cewar wani matashi.
A halin yanzu matasa na kira da babban murya ga sabuwar gwamnati akan ta duba lamarin ayyukan yi ga matasa.
Sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauki alwashin samar wa matasa ayyukan yi, a cikin manyan batutuwa uku da ya shata zai tunkara gadan-gadan a wa’adin shugabancinsa.
Masu fashin baki da masana tsaro sun alaqanta rashin ayyukan yi ga matasa a matsayin daya daga cikin dalilan dake saka su yin ayyukan asha, da tsawaita lokacin aure.