Kungiyar dake yaki da cin hanci da rashawa ta shirya taron bita domin duba illar da cin hanci ke yiwa kasa da al'ummarta.
Kungiyar tace matsalar cin hanci da rashawa su ne manyan annoba da suka addabi kasar a duka fannoni. Abdullahi Aliyu Katsina shugaban kungiyar yace cin hanci ke hana kasa ci gaba da gurbata rayuwar al'ummarta.
Yace suna nuna irin illar da cin hanci ke jawowa shi ya sa suke jawo hankalin gwamnati akan lamarin. Cin hanci na kashe mutane na kuma kashe kasa.
Yayi harsashen cikin 'yan watanni za'a ga canji a kasar to amma bukatun 'yan kasar sun yi yawa saboda komi na kasar ya lalace.
Wani masani yace cin hanci da rashawa suka yiwa kasar tarnaki har ma suna neman hana kasar yin nunfashi. Yace arzikin da Allah ya yiwa Najeriya idan ba cin hanci ba da kasar tana cikin kasashen da suka cigaba 'yan kasar kuma da suna cikin wadata.
Shi ma sakataren APC na kasa ya ce sace-sacen dukiyar Najeriya ba wani boyayyen al'amari ba ne a Najeriya.Yace kudin kasa an sace.Farashin man fetur kuma ya fadi. Gwamnatin PDP babu abun da tayi cikin shekaru 16 da tayi tana mulki. Basu habbaka harkokin noma ba ko harkokin ma'adanan kasa..An rasa yadda za'a yi anfani da albarkatun kasar a inganta rayuwar mutane saboda rashin shugabanci nagari.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.