Mai Shari’a ya bayyana cewa dalilin shi na zuwa Amurka shine ziyarar aiki da bude ido.
“A ko yaushe idan mutum yana aiki, zai yi kokari ya san hanyoyin da zai bunkasa aiki, saboda tafiya dai-dai da zamani. Kamar yadda ake ayyuka bayan komawa amfani da internet da kamfuta, da yadda ake amfani da nau’rorin zamani wajen daukar shaida, da kuma rubuta hukunci” a cewar Mai Shari’a Rufa’i.
Ya bayyana cewa sababbin hanyoyin gudanar da harkokin shari’a sun shigo wannan zamani, kuma alkalai a yammacin Afirka sun rungumi wannan sabon tsari.
Game da cin hanci da rashawa, Alkali Rufa’I yace “har yanzu dai, yadda shugaba yake, haka wanda yake shugabanta zai kasance. Lokacin da kana da shugaban dake kukan cin hanci, yana fada da cin hanci, yana yaki da cin hanci, kuma kaima ba zai barka ba idan kaci hanci, kaima dole zaka kyautata.”
“Idan aka tuna, inda muke fito wato Ma’aikatar Shari’a, an samu canji babba game da al-amuran cin hanci, da sakin ka’ida, da rashin adalci” inji Justice Rufa’i.
Alkalin ya yiwa Sashen Hausa na Muryar Amurka karin haske na cewa Ma’aikatar Shari’a ta Koli a Najeriya tayi gyara, kuma bata wasa ko kadan, a duk lokacin da aka samu wani koke, za’a kai matuka wajen bincike har sai an gane gaskiya.