WASHINGTON, DC —
A daidai lokacin da labari ya cika gari cewa shugaban jam'iyar PDP Alhaji Bamanga Tukur ya mika takardar murabus, sai kuma ga bayanin cewa kwamitin zartaswa na kasa kawai ne ke iya yanke shawara game da makomar Bamanga Tukur a matsayin shi na shugaban jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya:
Wakilin Sashen Hausa a Abuja Nasiru Adamu el-Hikaya ya ce har a lokacin da ya aiko da rahoto ana cikin rudamin cewa Bamanga ya mika takardar murabus, wasu kuma na cewa an tilasta mi shi yin murabus, ko da yake babu wata sanarwa daga gwamnati game da wannan al'amari, sai dai wta majiya mai tushe ta shaidawa Nasiru Adamu el-Hikaya cewa manyan jam'iyar ta PDP za su sake ganawa da misalin karfe shida a yau laraba domin su dauki matakin da za su dauka game da makomar Bamanga Tukur.