Shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Adamawa sun shirya taron gangami domin kada ya rasa kujerarsa a taron jam'iyyar da za'a yi yau. Wadanda suka shirya gangamin suna son su nunawa duniya cewa Bamanga Tukur ba abun yasarwa ba ne.
Lokacin gangamin tsohon karamin ministan kiwon lafiya Dr Aliyu Idi Hong ya ce ko sama da kasa zasu hade Bamanga Tukur na nan daram kan kujerarsa. Ya ce babu wani shugaban jam'iyyar da 'yan Najeriya suka yadda da shi sai Alhaji Bamanga Tukur. Ya ce muatanen dake burin sai an kori Bamanga Tukur a gaya masau yana nan daram babu inda zashi. In jishi talakawa na nan tare dashi. Laifin Bamanga Tukur shi ne tsayawar da ya yi cewa jam'iyya ta koma hannun talakawa abun da gwamnonin da suka fice daga jam'iyyar basa so ke nan.
A nata jawabin tsohuwar 'yar majalisar dattawa Sanato Grace Ben ta ce kan mage ya waye idanunta kuma sun bude. Ta ce ba za'a sake yin anfani da su ba. Ta ce taronsu ya nunawa kowa a Najeriya babu wata jam'iyya idan ba PDP ba.
Sanato Abubakar Gada mai ba Bamanga Tukur shawara ta fuskar harkokin siyasa ya wakilci shugaban jam'iyyar a taron. Ya ce ya zo ya ga abun da ya gani da idanunsa kana ya koma ya idar wa shugaban jam'iyyar sako.Ya ce abun da ya gani ya wuce magana. Ya ga mutanen Adamawa sun fito sun nuna suna nan bayan PDP.
Ga karin bayani.