Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Na Shirin Yiwa Majalisar Zartaswa Garambawul


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A kokarin tabbatar da cewa an sake zabarsa a zabe mai zuwa shugaban kasar Najeriya na shirin yiwa majalisar zartaswarsa garambawul

'Yan kwanakin da suka wuce ne shugaban kasa ya mikawa majalisar dattawa sunayen mutane tara da zasu tantance domin a basu mukaman ministoci.

Wadannan mutanen tara su ne zasu maye gurbin mutane taran da rikicin PDP ya lakume. Sai dai wata majiya ta ce shugaban zai jire duk ministocinsa ban da guda hudu kawai. Wadan da za'a bari su ne ministan yada labarai da ministan kudi da ministan aikin gona da ministan albarkatun man fetur. Duk sauran za'a saukesu. Haka ma kusan duka hadimansa za'a saukesu kodayake wasunsu na son komawa jihohinsu domin tsayawa zabe.

Wata majiya ta ce wadanda za'a nada mukamin zasu kasance 'yan siyasa zalla da zasu iya janyo hankulan 'yan Najeriya ga shugaban kasar domin su kada wa shugaba Jonathan da jam'iyyar PDP kuri'a.

A taron majalisar kolin da a ke yi kowace Laraba ana tsammanin shugaban zai rushe majalisar. Wato tana iya kasancewa ya saukar da ministocin a taron gobe. Kada a manta lokacin da ya karbi bakuncin 'yan jam'iyyar PDP daga arewa maso yamma ya shaida masu cewa zai mikawa majalisar dattawa sunayen sabbin ministoci.

Cikin wadanda a ke zaton za'a nada sun hada da tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Obasanjo shawara kan harkokin tsaro kodayake sai da ya shimfida wasu sharuda kafin ya amince a sa sunasa.

Babban jami'i a fadar shugaban kasa da ake kira chief of staff a turance ba zai tsallake wannan siradi ba. Ana kuma sa ran za'a dauko dan arewa ya maye gurbinsa.

An nemi ra'ayoyin 'yan Najeriya kan ko wannan sabon yukurin na shugaban kasa yana da faida ko kuma zai yi wani tasiri ga talakan Najeriya. Wasu sun ce manufar canza ministoci domin kawo canji ne mai ma'an amma a Najeriya bata sake zani. Za'a kori wasu yau, gobe a nada wasu amma ba za'a ga banbanci ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG