Hukumar ta ce kada su bari 'yan siyasa su yi anfani da su a matsayinsu na 'yan jarida wajen zafafa wutar rikici da kashe-kashe a kasar lokutan zabuka.Hukumar ta yi jawabin ne lokacin da a ke shirin zabukan gwamnonin a jihohin Ekiti da Osun a cikin wannan shekarar.
Kwamishanan zabe na kudu maso yamma Farfasa Layi Olurodi ya yi kiran a wajen taron masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa a Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyo. Ya ce ya zama wajibi 'yan jarida su ilimantar da al'umma kan harkokin zabe. Kada su bar ma INEC ita kadai ko 'yan siyasa. Su ma jam'iyyun siyasa da kungiyoyi ya kamata su taimaka wurin ilimantar da jama'a game da zabe.
Tsohon shugaban jaridar Punch Mr. Olalere Fagbola ya ce 'yan jarida jakadu ne wurin ilimantar da jama'a dangane da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da ma al'adun jama'a. Ya ce don haka ya kamata 'yan jarida su sani cewa suna da matsayi mai kyau na aiwatar da ilimantar da jama'a. Ya bukaci 'yan jarida su gudanar da aikinsu cikin tsarin aikin jarida ba tare da yin mitsitsi ba kana su kare gaskiya komi dacinta ba tare da jin tsoro ko fargaba ba.
Ga karin bayani.