Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Somaliya Ya Zamo Babban Alkalin Kotun Duniya


Abdulqawi Ahmed Yusuf
Abdulqawi Ahmed Yusuf

Alkali Abdulqawi Yusuf ya zamanto ‘dan kasar Somaliya na farko da ya taba zama shugaban babbar kotun duniya ta ICJ dake birnin Hague a kasar Netherlands.

Da yake magana ta wayar talho da sashen Somaliyanci na Muryar Amurka, Alkali Yusuf, ya ce “Na yi farin ciki da wannan zabe. kuma ina ji jikina wannan ya nuna min matsayina gurin abokan aiki na. hakan yasa nake matukar godiya garesu.”

Ya ci gaba da cewa “ina fatan bazan basu kunya ba wajen yin ayyukan da suka zabe ni na yi, domin nuna musu sun yi zabin shugaba mai kyau.”

Babbar kotun ICJ na da mambobi 15, kuma ita ce bangaren shari’a ta MDD. Ita ce ke yanke hukuncin karshe, watau tamkar kotun koli, a kan takaddama tsakanin kasashe biyu, kuma tana baiwa MDD shawara.

Yusuf, mai shekaru 69, ‘dan asalin garin Eyl dake gabar ruwa a Somaliya, yayi karatunsa a jami’ar Somaliya da jami’ar Florence da kuma jami’ar Geneva. Ya zamanto ‘dan nahiyar Afirka na uku da zai shugabancin babbar kotun.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG