Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanyoyin Kare Kai Daga Masu Kutse A Kan Yanar Gizo


A magnifying glass is held in front of a computer screen in this picture illustration taken in Berlin, May 21, 2013.
A magnifying glass is held in front of a computer screen in this picture illustration taken in Berlin, May 21, 2013.

Cikin shekarar da ta wuce ne wasu daga cikin masu amfani da shafin Facebook, suka fara samun sakon email da yake cewa, “domin dalilan kare bayananku, za a rufe shafinan ku” a ka ci gaba da cewa domin ka tabbatar da kaine mai wannan shafi ka danna nan domin ka sabunta bayanan ka.

Wannan sakon email dai ba Facebook bace ta aiko wa mutanen ba, ire iren masu kutse ne da satar bayanan mutane ke yiwa mutane wayo don kwashe sirrinsu, kamar irin su kalmomin sirru wato password da katunan banki. Yawancin lokuta irin wadan nan email na zuwa ga jama’a, inda ake amfani da sunan bankuna ko hanyoyin sadarwa, harma su bukaci mutane da su danna wani adireshi da zai shigar da su wani shafi domin kawar da matsalar, da zarar mutum ya shiga shafin ta nan ne zasu iya sace duk bayanan da mutum yake da cikin na’urar sa.

Kutse dai na faruwa a ko ina cikin duniyar nan. Wani kamfanin kare kutse mai suna Kaspersky yace cikin shekarar da ta wuce ya kare yin kutse har sau biliyan 800, kusan miliyan biyu daga cikin kutsen anyi kokarin satar kudi ne daga bankuna ta yanar gizo.

Hanyoyin da za’a bi don kare kai sun hada da:

Idan baka tabbas kan email da aka aiko maka kuma aka bukaci ka danna wani adireshi to kar ka soma yi, domin ka iya zama hatsari gareka.

Kada a cike wani fom da aka aiko maka ta hayar email, domin wanda ya aiko zai iya bin diddigin duk abinda ka rubuta a kwamfutar ka.

Ayi hankali da duk email din da ke tambayarka bayanan banki, ko kuma tace daga banki ne ana son ka sabunta bayanan ka. Domin wasu lokuta masu kutse kan aiko sako suce sakon gaggawa ne da bukatar mutum yayi abinda suka ce kawar da matsalar da suka ambata.

Hankali da duk wata gayyata ta hanyoyin sadarwa daga mutanen da baka sansu ba, domin sama da ‘daya cikin kutse biyar da akeyi yana faruwa ne ta kafar Facebook.

A kula da yadda masu kutse ke aiko sakonni domin wasu lokuta suka fara rubuta wasikar su ne kamar haka: “Dear Sir/Madam” wasu lokuta kan zone ta wani banki da mutum bashi wata alaka da su.

Kula da yadda suke aiko da sakonninsu domin sukan rubuta kalmomi ba dai dai ba, a rinka amfani da manhajojin kare kutse a duk na’urorin da ake amfani dasu wajen shiga yanar gizo.

XS
SM
MD
LG