An shirya a yau lahadin nan idan Allah ya yarda shugabanin arewaci da kudancin Sudan zasu gana a yayinda ake ci gaba da fafatawa akan iyakar kasashen biyu. A Addis Ababa baban birnin kasar Ethiopia aka shirya shugaba Omar Al Bashir zai gana da shugaban kudancin Sudan Salva Kir. Tsohon shugaban Afrika ta kudu Thabo Mbeki shine zai shiga tsakani. Kungiyar kasashen Afrika wadda ta dauki dawainiyar taron, tace shugabanin zasu tattauna batun janye sojojinsu daga yankin Abyei da ake rikici akansa da kuma yiwuwar a tura sojojin kiyaye zaman lafiya na Afrika a yankin.
A watan jiya sojojin arewacin kasar suka mamaye yankin Abyei mai arzikin mai, matakin daya sa dubban mutane suka arce daga yankin.
A wani wuri dabam kuma, yau fiye da mako guda ke nan da sojojin arewacin Sudan suke fafatawa da wasu kungiyoyi akan iyakar jihar Kordofan. A yau lahadi rundunar sojan arewacin Sudan ta musunta rahotranin dake cewa an harbor jiragen saman yakinta guda biyu a kudancin Kordofan. An shirya a watan yuli kudancin Sudan zai ayyana samun yanci.