Kungiyar masu masana’antu ta Najeriya ta ce a jihar Kano kawai mambobinta sun yi asarar fiye da naira biliyan dari biyu cikin cikin kasa da kwana 10 da yankin arewacin Najeriya ya kasance babu wutar lantarki.
Yanzu dai kimanin makonni biyu kenan babu hasken wutar lantarki a daukacin yankin na arewacin Najeriya birni da karkara.
Da farko dai, kamfanin samar da lantarki na kasar wato TCN ya ce bai iya gano musabbabin wannan matsala ba, amma daga bisani mahukuntan kamfanin sun ce wasu ‘yan ta’adda ne suka lalata layukan da ke kawo lantarkin zuwa arewa daga yankin kudancin kasar a tsakiyar wasu dazuka na jihar Benue.
Yanzu haka manyan da kananan ‘yan kasuwa, musamman masu masana’antu a dukkanin jihohin arewa 19 na Najeriya na ci gaba da kirga asara da kuma dakatar da ma’aikata saboda rashin lantarki.
Alhaji Sani Hussaini Birnin Kudu, mamba ne a kwamitin koli na kungiyar masu masana’antu ta Najeriya wato MAN, ya ce tuni masu masana’antu da dama a sassan Arewacin Najeriya suka dakatar da ma’aikatan su zuwa lokacin da al’amura za su daidaita kuma ya zuwa yanzu, mambobin kungiyar sun yi asarar kudi daga Naira biliyan 200 zuwa biliyan 500.
Sai dai mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibril ya ce shugabancin majalisar dokoki ta kasa tana aiki tare da fadar shugaban kasa ta hannun mai bai wa shugaban kasar shawara akan harkokin tsaro domin magance wannan kalubale.
Tun ba yanzu ba, masana harkokin tsaro an karar da mahukuntan Najeriya kan matakan da ya kamata a dauka domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda a dazuka.
Da yake tsokaci kan harkar tsaro, Detective Auwalu Bala, guda cikin masana da ke sharhi akan harkokin tsaro a Najeriya, ya ce kafa dakarun tsaron daji kuma a ba su horo na musamman na daga cikin hanyoyin da za’a bi domin tabbatar da tsaro a dukkanin dazukan da ke fadin Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:
Dandalin Mu Tattauna