Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TCN Ya Hada Kai Da Ofishin Ribadu Don Samar Da Tsaro A Wajen Da Ake Gyaran Wutar Lantarki


Ma'aikata na gyara a wasu turakun wutar lantarki a Najeriya (Hoto: X/TCN)
Ma'aikata na gyara a wasu turakun wutar lantarki a Najeriya (Hoto: X/TCN)

Kamfanin na TCN ya kore wasu rahotannin da ke nuni da cewa babu ranar kammala aikin gyaran wutar.

Kamfanin Samar da Wuta na TCN a Najeriya, ya ce ya hada kai da ofishin mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan harkar tsaro Malam Nuhu Ribadu a kokarin da yake yi na gyara katsewar wutar lantarki da ta shafi wasu jihohin Arewacin kasar.

A ranar Talatar da ta gabata wasu bata-gari suka lalata babban layin Shiroro-Mando da ke ba yankin wutar lantarki a cewar TCN.

A mataki na wucin gadi kamfanin ya karkata akalar wutar zuwa layin Ugwuaji-Apir mai daukar nauyin 330kv – amma shi kuma ya katse.

“Muna kan yin hadaka tare da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro don ya yi aiki tare da injiniyoyinmu saboda a kai ga yankin da aka lalata wutar don a gyara.” In ji Kakakin TCN Ndidi Mbah.

Mai Bai wa Shugaban Najeriya Shawara Kan Lamarin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu
Mai Bai wa Shugaban Najeriya Shawara Kan Lamarin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu

Kazalika kamfanin ya kore wasu rahotannin da ke nuni da cewa babu ranar kammala aikin gyaran wutar.

“Babbar Darektar kamfanin na TCN mai zaman kansa, Nafisatu Ali ta jaddada cewa zuwa yankin don gyara wutar ba zai yiwuwa ba duba da matsalar tsaro da yankin yake fama da shi.” Sanarwar ta ce wacce kamfanin ya fitar a ranar Lahadi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG