Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Na Shirin Kirkirar Wani Tsarin Samar Da Lantarki Mai Amfani Da Hasken Rana A Arewacin Kasar


Ma'aikata na gyara a wasu turakun wutar lantarki a Najeriya (Hoto: X/TCN)
Ma'aikata na gyara a wasu turakun wutar lantarki a Najeriya (Hoto: X/TCN)

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin gaggauta aikin gyara domin dawo da hasken lantarki ga shiyar arewacin Najeriya.

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana kokarin samarda wani faffadan tsarin lantarki mai zaman kansa ga kowacce daga cikin jihohin arewacin kasar 19.

Ministan Lantarki Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da Shugaban Najeriya Bola Tinubu a jiya Litinin a Abuja.

A cewarsa, shugaban kasar ya bada umarnin gaggauta aikin gyara domin dawo da hasken lantarki ga shiyar arewacin Najeriya.

Shiyar arewacin Najeriya ta afka cikin duhu tsawon kwanaki sakamakon lalata wasu daga cikin layukan dakon lantarkin, abinda ya haddasa damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki a yankin dama wajensa.

Adelabu ya kara da cewar, “munyi imanin cewar hanya mafi dacewa ta samarda lantarki da za’a dogara dashi kuma wanda ba zai dauke ba a shiyar arewacin najeriya ita ce ta tsarin rarraba wuta ta yadda za’a sanyawa kowacce daga jihohin yankin 19 tsarin zukar hasken rana. Za’a killace kowace daga cikin jihohin 19 kuma za ta zamo mai dogaro da kanta.

“Mun yi nisa akan haka kuma mun samu ‘yan kwangila da cibiyoyin hada-hadar kudin da suka nuna sha’awar samar da tsarin lantarki mai karfin megawatts 100 ga kowacce daga cikin jihohin arewacin Najeriya 19 wanda za’a soma da samar da megawatts 50 kana daga bisani a kara shi zuwa megawatts 100.

“Muna aikin kafa wani faffadan tsarin samar da lantarki da zai kasance madogara kuma zabi na daban. Duk lokacin da babban layin lantarkin kasa ya samu matsala, za’a samu wani layin na daban da za’a iya tura wutar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG