Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Jami'in Diflomasiyyar Rasha Ya Yi Alkawarin Karin Tallafin Soja Ga Burkina


Ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergey Lavrov lokacin ziyararsa Burkina Faso
Ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergey Lavrov lokacin ziyararsa Burkina Faso

Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya yi alkawarin karin goyon baya ga kasar Burkina Faso wajen yakar kungiyoyin 'yan ta'adda a yayin wata ziyara da ya kai yammacin Afirka a wani yunkuri na cike gibin da kawayen kasashen yammacin Turai suka bari yankin.

WASHINGTON, D. C. - Sergey Lavrov ya yi magana a wani taron manema labarai a Ouagadougo babban birnin kasar jiya Laraba, yayin da ya yada zango a kasa ta uku a ziyararsa ta baya-bayan nan a Afirka, bayan ziyarar kasashen Guinea da Jamhuriyar Congo.

Rasha na neman kara samun goyon baya daga yankin a daidai lokacin da Moscow ke mamaye Ukraine gaba daya. Yawancin kasashen Afirka a cikin 'yan shekarun nan sun nuna rashin jin dadinsu ga abokan huldarsu na yammacin Turai kamar Faransa da Amurka.

"Masu koyarwa na Rasha suna aiki a nan kuma adadinsu zai karu," in ji Lavrov, ya kara da cewa, Rasha tana taimakawa wajen horar da sojoji da jami'an tsaro na Burkina Faso.

"Mun kawo kuma za mu ci gaba da samar da kayan aikin soji don taimakawa Burkina Faso karfin tsaro, da kuma ba ta damar kawar da sauran kungiyoyin ta'addanci."

Lavrov ya ce ya yaba da matsayin "manufofi da adalci" na Burkina Faso kan yakin Ukraine. "A namu bangaren, a shirye muke mu ba da goyon bayanmu don yin adalci ga 'yan Afirka da ke kokarin 'yantar da kansu daga tasirin mulkin mallaka."

Kasar Burkina Faso mai mutane miliyan 20, ta yi fama da tashe-tashen hankula a cikin shekaru 8 da suka gabata sakamakon tashin hankalin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da ke da alaka da Al-Qaida da kungiyar IS, da kuma fadan da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da mayakan.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG