Sakataren hukumar PURC Dakta Ishmael Ackah, shine ya sanarwa da manema labarai matakin hukumar na kara kudin ruwa da wuta a birnin Accra.
Hukumar ta daura alhakin wannan kari bisa hauhawar farashin kayayyayaki da faduwar darajar kudin kasar Sidi, lamarin da ya sa hukumar dake samar da ruwa GWCL da takwararta ta wutar lantarki ECG suka nemi a kara fiye da kashi dari kan farashin da ake sayarwa a yanzu.
Ana sa ran wannan karin zai fara aiki daga ranar daya ga watan Satumba bana, inda al’ummar kasar za su biya karin sama da kashi 20 na kudin ruwa da wutar lantarki.
Shugaban kungiyar hadin gwiwar masu harkar kasuwanci a Ghana GNCCI, Mista Mark Badu Aboagye, ya ce kara kudin wuta da ruwa a wannan lokaci zai kara haddasa hauhawar farashin kayayyaki yayin da kasar ke fama da matsalar tsadar rayuwa.
"Hauhawar farashin kayayyaki yayi sama sannan kuma ga karin kudin wuta da ruwa ina ganin lokacin kara kudin bai dace da yanayin da ake ciki ba. Kuma karin ya yi yawan gaske a don haka ya kamata gwamnati ta yi kokari ta rage"
Masanin tattalin arziki Najeeb Ibn Hassan, na ganin karin kudin wuta da ruwa a yanzu zai iya yin mummunan ta'asiri a kan al’umma ganin yadda zai iya jefa masu kananan sana’o’i cikin matsanancin hali.
Mallam Ibn Hassan ya baiwa gwamnati shawara da ta yi kokarin samun kudi, domin ta samu hanyar fitar da kasar daga cikin yanayin da take.
Hukumar PURC mai daidaita farashin kayayyaki a kasar ta jadaddda cewa shiga tsakani da ta yi shine ya sa ba a kara kudi mai yawa ba, ganin yadda hukumomin samar da wuta da ruwa ke neman kara fiye da kashi dari.
Domin karin bayani saurari rahotan Hamza Adam.