Gwamnatin Pakistan ta sanar da cewar zata gurfanar da shugabanin wata Jam’iyyar Musulunci, kan laifin cin amanar kasa da Ta’addanci.
Wannan zargin ya faro ne tun a watan Nuwamba da aka gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da hukuncin kotun kolin kasar, da ta wanke wata mata Kirista da laifin yin kausasan lafuzza ga Annabin Rahama Muhammad (SAW).
Wanda a baya aka yanke mata hukuncin kisa, kungiyar Tehreek-i-Labbaik Pakistan (TLP) kungiyar addini, wadda da ga baya ta rikide ta koma kungiyar siyasa ita ta shirya zanga-zangar.
Ministan yada labarai Fawad Chaudhry, ya shaida ma manema labarai jiya Asabar, cewar an kama mutane sama da 3,000 mambobin kungiyar ta TLP suna nan tsare, harda shugaban kungiyar Khadim Hussain Rizvi.
Ministan yace akasarin kamen anyi shine a Lardin Punjab inda kungiyar tafi karfi.
Facebook Forum